logo

HAUSA

Ramaphosa: Afirka ta kudu ta amfana da kungiyar BRICS

2021-09-14 09:45:18 CRI

Ramaphosa: Afirka ta kudu ta amfana da kungiyar BRICS_fororder_210914-yaya-2-Afirka ta kudu

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasarsa ta ci gajiyar kasancewar mambar kungiyar BRICS, cikin shekaru goma da suka gabata.

Ya ce, shiga cikin kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa, ya bunkasa matsayin kasar Afirka ta kudu a matsayin muhimmiyar kasa da tattalin arzikinta ke bunkasa a duniya. Ya kara da cewa, hakan ya kuma baiwa kasar damar samun manufofi da kwarewar fasaha na manyan kasashe masu tasowa, baya ga damar samun tallafin sabon bankin ci gaba.

Ramaphosa ya kuma lura da habakar alakar kasuwanci musamman tsakanin Afirka ta kudu da kasarshen Sin da Indiya. A don haka, ya yaba da hadin kan da kasarsa take samu daga sauran kasashen kungiyar BRICS, a fannonin samar da kayan kariya, da hadin gwiwa game da samar da alluran riga kafi da ma yadda ake raba su. (Ibrahim Yaya)