logo

HAUSA

Firsunoni 240 sun tsere daga gidan yarin jihar Kogi

2021-09-13 21:17:48 CRI

Wasu rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla firsunoni 240 ne suka tsere daga gidan yarin Kabba dake jihar Kogi, a shiyyar tsakiyar kasar, biyowa bayan harin wasu masu dauke da makamai a daren jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da aukuwar hakan, kakakin hukumar dake lura da gidajen gyaran hali ta Najeriya NCoS, Mr. Francis Enobore, ya ce maharan sun kutsa kai cikin gidan yarin, bayan musayar wuta da dakarun dake tsaron sa, kana suka kubutar da firsinoni 240.  (Saminu)