logo

HAUSA

Wai hari da ’yan bindiga suka kai kan sansanin soja a Zamfara ya hallaka sojoji 12 tare da jikkata 3

2021-09-13 10:17:17 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, da misalin karfe 10 da rabi na safiyar ranar Asabar din da ta gabata, wasu gungun ’yan bindiga dauke da makamai, sun kai hari kan wani sansanin soja mai nisan kilomita 80 kudu da Gusau, babban birnin jihar Zamfara, lamarin da ya haddasa kisan jami’an sojan sama 9, da ’yan sanda 2 da sojan kasa 1 kana wasu 3 suka jikkata. Bugu da kari, ’yan bindigar sun kwace makamai da kayayyakin aiki daga jami’an da suka kashe tare da kona wani bangare na sansanin.

A kwanakin nan, gwamnatin Najeriya ta kara kaimi wajen kai farmaki kan ’yan fashi a arewa maso yammacin kasar. A lokaci guda kuma, a kokarin katse hulda da ’yan fashin, hukumar sadarwa ta kasar, ta bayar da umarnin rufe hanyoyin sadarwar wayar hannu a duk fadin jihar Zamfara, tun daga ranar 3 zuwa 17 ga watan Satumba. A wani mataki na hana ’yan fashi da su yi amfani da hidimomi na sadarwa, a ranar 11 ga watan na Satumba, an tsawaita dokar hana toshe hanyoyin sadarwa zuwa kananan hukumomi 13 na jihar Katsina dake kusa da jihar Zamfara. (Ibrahim)