logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun sako gwamman daliban sakandaren Kaya ta jihar Zamfara

2021-09-13 21:21:38 CRI

Wata majiyar jami’an tsaro ta bayyana sakin gwamman daliban makarantar babbar sakandaren Kaya, dake karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, a jiya Lahadi, inda tuni aka sada daliban da iyalan su.

Majiyar dai ba ta bayyana takamaiman adadin daliban da aka saka, da kuma hanyoyin da aka bi wajen kubutar da su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su ba.

A ranar 1 ga watan nan na Satumba ne dai wasu mahara da ake kyautata zaton masu sace mutane domin neman kudin fansa ne, suka yi awon gaba da daliban sakandaren ta Kaya su 73, kamar dai yadda wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar. (Saminu)