logo

HAUSA

Tsohon firaministan Madagascar: Bai kamata a siyasantar da batun asalin COVID-19 ba

2021-09-12 17:17:27 CRI

Binciken asalin cutar COVID-19 batu ne mai sarkakiya wanda kuma ya shafi bin matakan kimiyya, kamata yayi a yi Allah wadai da siyasantar da batun, tsohon firaministan kasar Madagascar Norbert Ratsirahonana, ya bayyana hakan a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ratsirahonana, wanda shi ne babban jami’in jam’iyyar IRD mai mulkin kasar, yace jam’iyyarsa ta yi Allah wadai da dukkan yunkurin da wasu kasashen duniya ke yi na neman siyasantar da wannan batu da kuma yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti wajen alakanta ta da asalin annobar.

Ratsirahonana yace, gano asalin annobar COVID-19 zai iya dakatarwa da kuma kawar da yaduwar annobar.

A cewar Ratsirahonana, jam’iyyar IRD tana maraba da kokarin da kasar Sin ke yi wajen kawar da annobar a cikin gidan kasar har ma da kasa da kasa.(Ahmad)