logo

HAUSA

Tawagar wakilan ECOWAS ta je Guinea domin tattaunawa da sojojin juyin mulki

2021-09-11 16:00:44 CRI

Tawagar wakilan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ta je Conakry, fadar mulkin kasar Guinea a jiya Juma’a, domin tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar tare da tsare shugaba Alpha Conde.

Shugaban hukumar ECOWAS Jean-Claude Brou, shi ne ya jagoranci tawagar, wadda ta kunshi ministocin harkokin wajen kasashen Ghana da Togo da Burkinafaso, da jakadan tarayyar Najeriya dake Guinea, da wakilin ECOWAS dake wakilci a Guinea da sauransu.

Bayan tattaunawar da suka yi, Jean-Claude Brou ya bayyana wa manema labarai cewa, tattaunawar da tawagarsa ta yi da sojojin ta samu babban sakamako, kuma shugaba Alpha Conde na cikin koshin lafiya. Ya kara da cewa, bayan komawarsu, za su gabatar da abubuwan da suka tattauna ga shugabannin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Rahotannin na cewa, tuni tawagar ta riga ta tashi daga Conakry da yammacin jiya.

A ranar 5 ga wata ne aka yi boren siyasa a kasar Guinea, inda sojojin da suka yi juyin mulki suka sanar da cewa, sun tsare shugaban kasar Alpha Conde tare kuma da rusa gwamnatinsa. Daga baya kuma, suka bayyana cewa, za su kafa gwamnatin hadin kan al’ummun kasar.(Jamila)