Dabarun Xi za su ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS
2021-09-10 19:28:42 CRI
A yammacin jiya Alhamis 9 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ganawar shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS karo na 13 ta kafar bidiyo, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, tare kuma da gabatar da dabarun ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashen a fannoni biyar.
Dabarun da shugaba Xi ya gabatar sun hada “nacewa kan hada kai domin kara karfafa hadin gwiwar kiwon lafiyar jama’a”, da “nacewa kan adalci domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa wajen samar da allurar rigakafin cutar COVID-19”, da “nacewa kan manufar moriyar juna domin kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki”, da “nacewa kan adalci domin kara karfafa hadin gwiwar tsaron siyasa”, da kuma “nacewa kan koyi da juna domin kara karfafa cudanyar al’adu”, wadannan dabaru ba ma kawai sun mai da hankali kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren kandagarkin annoba ba, har ma sun tsara tsarin farfadowar tattalin arziki da hadin gwiwar siyasa da kuma cudanyar al’adu, ana iya cewa, dabarun da shugaba Xi ya gabatar sun nuna cewa, kasar Sin babbar kasa ce dake sauke sauyin dake bisa wuyanta.
An lura cewa, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta samar da allurar rigakafin COVID-19 da yawansu ya kai biliyan 1 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100, kuma za ta ci gaba da samar da allurar da yawansu zai kai biliyan 2 ga sauran kasashen duniya a cikin shekarar da ake ciki. Ban da haka, kasar Sin ta sanar da cewa, ban da tallafin kudi dalar Amurka miliyan 100 da ta samar wa shirin COVAX, za kuma ta samar da karin allurai miliyan 100 ga kasashe masu tasowa kyauta kafin karshen shekarar 2021 da ake ciki.(Jamila)