logo

HAUSA

’Yan bindiga sun sace ma’aikata 3 na tsohon shugaban Nijeriya

2021-09-10 10:05:45 CRI

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kaddamar da farautar wadanda suka sace hadimai 3 na tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, a jihar Ogun dake kudu maso yammacin kasar.

Rundunar ta ce tuni a ranar Laraba aka tura jami’an sashen yaki da satar mutane domin binciken yankunan da aka sace mutanen a kewayen kauyen Sesari dake yankin karamar hukumar Obafemi-Owode ta jihar.

Kakakin rundunar dake jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Xinhua ta wayar tarho cewa, mutanen sun kasance ma’aikata a gonar tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo. (Fa’iza Mustapha)