logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun kama wani da ake zargin kusa ne a kungiyar BH

2021-09-10 09:59:02 CRI

Sojojin Nijeriya sun kama wani da ake zargin kusa ne a kungiyar BH_fororder_210910-Faeza 1

Sojojin Nijeriya sun cafke wani da ake zargin kusa ne a kungiyar BH, tare da wasu abokan huldarsa biyu, biyo bayan wani samame da suka kai maboyar kungiyar dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Onyema Nwachukwu, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, sojoji sun kama wanda ake zargin, Yawi Modu, dake cikin jerin wadanda rundunar ke nema, yayin samamen da suka kai kan hanyar Damboa zuwa Wajiroko ta jihar Borno.

Sai dai, bai bayyana yaushe da kuma yadda sojojin suka cafke dan ta’addan ba, amma ya ce an kai wani samamen maboyar kungiyar dake jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Borno.

Yayin samamen, sojojin sun gano wani wurin tara kayayyakin hada ababen fashewa da kungiyar ke amfani da su a yankunan kananan hukumomin Damboa ta jihar Borno da kuma Gashua ta jihar Yobe. (Fa’iza Mustapha)