logo

HAUSA

Matasan Afrika sun lashe kyauta fasahar kirkire kirkiren aikin gona

2021-09-09 10:57:02 CRI

Matasan Afrika sun lashe kyauta fasahar kirkire kirkiren aikin gona_fororder_0909African leaders-Ahmad

Wasu matasa biyu da suka nuna bajintar kirkire-kirkire ’yan kasashen Kenya da Najeriya, sun samu lambar yabo na lashe tsabar kudi da ya kai dala miliyan 1.5 bisa fasahar da suka kirkira irinta ta farko wacce za ta haifar da sauye-sauyen bunkasa ayyukan noma a nahiyar Afrika.

Matasan da suka lashe gasar fasahar aikin gonar, wanda gidauniyar raya ci gaban kasa da kasa wato Heifer International, ta dauki nauyin shiryawa, an sanar a lokacin taron kolin AGRF a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Daga cikin matasan biyu da suka lashe gasar ta fasahar gona ta 2021 ta Afrika, wato (AYuTe), akwai Nnaemeka Ikegwuonu, wanda ya kafa kamfanin ColdHubs, wani kamfani ne a Najeriya wanda ke samar da makamashi ta hanyar amfani da hasken rana, yana samar da wuraren ajiya masu sanyi wanda manoma za su iya adana kayan lambu da ganyayyaki.

A cewar Ikegwuonu, ya kafa kamfanin ColdHubs ne don samar da hidimomin wuraren ajiya masu sanyi wanda ake biya kafin bayar da hidimar a budaddun kasuwanni, lamarin da ke bayar da dama ga ’yan kasuwa inda za su iya adana danyun kayayyakin amfanin gona daga kwanaki biyu har zuwa 21, sannan fasahar tana rage dunbun hasarar da kananan manoma ke tafkawa da kashi 50% bayan girbe amfanin gonarsu. (Ahmad)