logo

HAUSA

Masana: Manufar bunkasa abinci na kasar Sin lokacin fama da annoba ya ja hankalin Afrika

2021-09-09 10:46:53 CRI

Masana: Manufar bunkasa abinci na kasar Sin lokacin fama da annoba ya ja hankalin Afrika_fororder_0909China-Ahmad

Kokarin da kasar Sin ke yi wajen kiyaye manufofinta na samar da abinci da bunkasa aikin gona a yayin da ake fama da annobar COVID-19 ya kasance babban darasi ga kasashen Afrika, kamar yadda masana suka bayyana.

Yayin jawabi a gefen taron kolin AGRF na 2021 a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, masana sun bayyana cewa, ya kamata kasashen Afrika su rungumi ingantaccen tsarin da kasar Sin ke amfani da shi wanda ya kunshi amfani da tsarin ciniki ta intanet domin rage illolin da annobar ke haifarwa ga fannin ayyukan gona da hada hadar kasuwancinsu.

Fadel Ndiame, mataimakin shugaban gamayyar kungiyar bunkasa ayyukan gona ta Afrika, AGRF, dake da ofishinta a Nairobi, ya ce kamata ya yi fannin aikin gona ya zamo wani muhimmin jigo na hadin gwiwar Sin da Afrika, ya kara da cewa, fannin yana da matukar alfanu wanda ya hada da farfado da tattalin arzikin mazauna karkara, samar da abinci, da guraben ayyukan yi dogaro da kai ga matasa. (Ahmad)