logo

HAUSA

Masanin kwayoyin cututtuka na Najeriya ya bukaci a gudanar da aikin binciken gano asalin COVID-19 bisa kimiyya

2021-09-08 13:51:20 CRI

Masanin kwayoyin cututtuka na Najeriya ya bukaci a gudanar da aikin binciken gano asalin COVID-19 bisa kimiyya_fororder_1271709975001694217

Masanin kwayoyin cututtuka na Najeriya kana shugaban kwamitin kwararru na kasar dake bibiyar cutar COVID-19 Oyewole Tomori, ya bayyana cewa kamata ya yi a daina siyasantar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar Covid-19, maimakon haka, a mayar da hankali kan shaidun kimiyya na zahiri.

Oyewole Tomori, ya shaidawa manema labarai cewa, yana da wahala a tantance asalin kwayar cutar. Ya kuma yi imanin cewa, a halin yanzu kamata ya yi a yi watsi da tunanin da wasu ke yi wai, kwayar cutar ta bulla ne daga dakin bincike, har sai an samu kwararan shaidu dake tabbatar da hakan, amma idan har hakan ya zama wajibi, kamata ya yi a gudanar da aikin binciken a duniya baki daya, karkashin jagorancin WHO, ba kuma tare da matsin lamba daga Amurka ba.