logo

HAUSA

Sojojin Guinea sun sanar da goyon bayan kwamitin hadin kai da cigaban kasar

2021-09-08 10:57:14 CRI

Sojojin Guinea sun sanar da goyon bayan kwamitin hadin kai da cigaban kasar_fororder_e4dde71190ef76c6f9835f0c1aaae8f3ae51678d

Jami’an sojojin kasar Guinea sun gudanar da tattaunawa da madugun juyin mulkin kasar Mamady doumbouya a jiya Talata, inda suka bayyana goyon bayansu ga sojojin da suka shirya juyin mulki da ma kwamitin hadin kai da cigaban kasa da suka kafa.

Sidi Yaya Camara, birgediya na sojojin saman kasar Guinea, kana babban jami’in ma’aikatar tsaron kasar, ya bayyana a yayin taron cewa, suna goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulkin bisa la’akari da kiyaye moriyar kasar da ma hana kutsen kasashen waje, kuma suna fatan sojojin za su cigaba da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Ahmad)