logo

HAUSA

Minista Shava: Bai kamata a zargi Sin kan barkewar annobar Covid-19 ba

2021-09-08 16:08:42 CRI

Minista Shava: Bai kamata a zargi Sin kan barkewar annobar Covid-19 ba_fororder_a05-China Not To Blame For Covid Outbreak-0908

Shafin intanet na New Zimbabwe.com ya ba da rahoto a ranar 4 ga watan Satumba cewa, ministan harkokin wajen kasar Zimbabwe, Fredrick Shava, ya ce kasar Zimbabwe ta bukaci al’umma da su yi la’akari da sakamakon da tawagar kwararrun masana kimiyya na hukumar lafiya ta duniya WHO suka samu, inda suka wanke kasar Sin daga zarginta da haddasa barkewar annobar Covid-19.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga jami’an diflomasiyya game da batun cutar Covid-19 a birnin Harare a wannan mako.

Shava ya ce, kamata ya yi mutane su amince da kwararrun WHO wanda suke ganin cewa ba zai yiwu a ce annobar Covid-19 an samar da ita ne a dakin gwaje gwaje a birnin Wuhan, na kasar Sin ba.

Zimbabwe tana bukatar dukkan al’umma da su yi la’akari da batun kimiyya. A cewarsa, wajibi ne a amince da gwajin kimiyya, ko kuma hujjojin da aka samu ta hanyar binciken kimiyya domin kafa hujja da su.

Shava ya ce, bai kamata a dorawa kasar Sin alhakin barkewar annobar Covid 19 ba. (Ahmad)