logo

HAUSA

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea sun saki fursunonin siyasa da ake tsare da su

2021-09-08 20:03:03 CRI

Rahotanni daga kasar Guinea na cewa, sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, Sun saki fursunonin siyasa da ake tsare da su. An yanke wannan shawara ce a jajiberin taron kolin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), wanda zai tattauna juyin mulkin da sojoji suka yiwa shugaban kasar Guinea Alpha Conde.

A yammacin ranar Litinin 6 ga wata ne, aka saki fursunonin siyasa 79, kuma galibin wadanda aka sakin, suna da alaka da mutanen da aka kama a lokacin zanga-zanga da kuma mambobin kungiyar dake rajin kare kundin tsarin mulkin kasar (FNDC).(Ibrahim)