logo

HAUSA

Daliban Kamaru sun koma makarantu tare da bin matakan kariya daga COVID-19

2021-09-07 15:03:11 CRI

Daliban Kamaru sun koma makarantu tare da bin matakan kariya daga COVID-19_fororder_src=http---p9.itc.cn-q_70-images03-20201006-fabb44afcbd44722841f78d275a92c24.jpeg&refer=http---p9.itc

A jamhuriyar Kamaru an sake bude makarantun firamare da na sakandare a ranar Litinin tare da cigaba da daukar kwararan matakan kariya daga cutar COVID-19.

Laurent Serge Etoundi Ngoa, ministan ilmi a matakin farko na kasar, ya fadawa ‘yan jaridu a Yaounde babban birnin kasar yayin fara sabon zangon shekarar karatu cewa, tun a shekarar bara, an dauki ingantattun matakai a makarantun kasar domin yaki da annobar COVID-19. An sake karfafa wadannan matakai. Kuma an yi odar karin kayayyakin yaki da cutar ta COVID-19 da suka hada da takunkumin rufe fuska inda aka rarraba su zuwa dukkan shiyyoyin kasar.

Kimanin yara dalibai miliyan biyu ne suka koma makarantu a ranar farko da aka bude makarantun a kasar ta tsakiyar Afrika, kamar yadda jami’an sashen ilmin kasar suka bayyana.(Ahmad)