logo

HAUSA

Wasannin kwaikwayon kasar Sin na kara samun karbuwa a Ghana

2021-09-07 20:04:22 CRI

Wasannin kwaikwayon kasar Sin na kara samun karbuwa a Ghana_fororder_startimes

Sama da mutane miliyan 30 ne dake kasar Ghana a yammacin Afirka, suna da zabi na kallon shirye-shirye masu kayatarwa, daga cikinsu shi ne, wasannin kwaikwayon kasar Sin dake samun karbuwa.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Han Junyong, darektan rukunin kamfanin Star Times na kasar Sin dake Ghana, ya bayyana cewa, wasannin kwaikwayon talabijin na kasar Sin, na kara samun karbuwa a kasar Ghana.

Han ya ce, wani binciken kasuwa da suka gudanar ya nuna cewa, ‘yan kasar Ghana, ba kawai suna son wasannin kwaikwayon gargajiyar kasar Sin ba, har da na zamani, wadanda ke nuna yanayin rayuwar birane, musamman wadanda ke kunshi da wasan ban dariya da tsarin zamantakewar iyali.(Ibrahim)