logo

HAUSA

’Yan tawayen kasar Guinea sun yi shelar tsare shugaban kasar

2021-09-06 10:31:38 CRI

’Yan tawayen kasar Guinea sun yi shelar tsare shugaban kasar_fororder_微信图片_20210906103056

A jiya Lahadi, sojojin kasar Guinea da suka yi bore sun yi shelar tsare shugaban kasar Alpha Conde tare da rushe gwamnati. MDD da Tarayyar Afirka (AU) da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da ma sauran kungiyoyin duniya sun fitar da sanarwa, inda suka yi Allah wadai da yadda aka karbi ikon mulki ta hanyar nuna karfin tuwo, tare da bukatar sojojin su saki Alpha Conde nan da nan.

’Yan tawayen kasar Guinea sun yi shelar tsare shugaban kasar_fororder_微信图片_20210906103103

A wannan rana kuma, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana ta kafar sada zumunta cewa, yana matukar mai da hankali kan halin da ake ciki a kasar, kuma yana Allah wadai da yadda aka kwace mulkin gwamnati, inda ya bukaci sojojin su saki Alpha Conde ba tare da bata lokaci ba. (Lubabatu)