logo

HAUSA

Firaministan Libya: Tilas ne a hukunta dakarun da suka ta da yaki a Tripoli

2021-09-05 16:50:26 CMG

Firaministan Libya: Tilas ne a hukunta dakarun da suka ta da yaki a Tripoli_fororder_0905-Tripoli-Ahmad

Firaministan kasar Libya Abdul Hamed Dbeibah, ya sanar cewa, tilas ne a hukunta dakarun tsaron da suka gwabza fada a kudancin Tripoli a ‘yan kwanakin da suka shude.

A sanarwar da gwamnati ta fitar bayan kammala tattaunawa da manyan jami’an tsaro da jami’an sojojin gwamnartinsa a Tripoli, babban birin kasar, Dbeibah ya ce, ba za a laminci laifin da aka aikata ba, kuma tilas ne a hukunta dukkan mutanen da suka ba da gudunmawa wajen ta da rikicin.

Dbeibah ya ba da umarnin kafa kwamitin binciken kwa-kwaf don gano gaskiyar abinda ya faru wanda kuma zai mika rahotonsa a cikin wannan mako, domin daukar dukkan matakan da suka dace game da lamarin.

Fada ya barke ne a tsakanin dakarun tsaron gwamnatocin biyu a daren Alhamis a kusa da sansanin sojoji dake kudancin Tripoli, inda ba a bayyana adadin dakarun da rikicin ya rutsa da su ba.

Fadar shugaban kasar Libya ta bayar da umarni a ranar Juma’a cewa, a gaggauta tsakaita bude wuta kuma dukkan dakarun tsaron dake yaki da juna su koma helkwatocinsu.(Ahmad)

Ahmad