logo

HAUSA

An ji karar harbe harbe a babban birnin kasar Guinea

2021-09-05 20:51:55 CRI

Mazauna Conakry, babban birnin kasar Guinea, sun bayyana a yau 5 ga wata cewa, sun ji wata mummunar karar harbe harben bindiga a birnin da misalin karfe 8 na safiya, agogon kasar.

Mazaunan sun ce an ji karar harbe harben ne daga bangaren da fadar shugaban kasar Guinea da ma’aikatar tsaron kasar suke wanda aka shafe mintoci 20 ana jin karar. Akwai barikin sojojin a yankin.

Ya zuwa yanzu, jami’an kasar Guinea ba su ce komai ba game da lamarin. Sai dai sojojin kasar Guinea sun kafa shingayen bincike a yankunan da lamarin ya faru, kana an haramtawa mazauna yankunan fita na wucin gadi.(Ahmad)