logo

HAUSA

AU ta horar da jami’an ’yan sandan Somaliya 27 don sanya ido a zaben kasar

2021-09-03 10:39:07 CRI

AU ta horar da jami’an ’yan sandan Somaliya 27 don sanya ido a zaben kasar_fororder_0903-Ahmad2-Somaliya

Shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliya (AMISOM) ya sanar da cewa, ya kammala aikin horar da jami’an ’yan sandan Somaliya 27 na tsawon kwanaki 5 game da yadda za su sanya ido kan zabukan kasar dake gudana.

Jami’i mai bayar da shawarwari da yin sauye sauye da bunkasa cigaba na tawagar AMISOM, Agapitus Ecotu, ya ce dakarun ’yan sandan Somaliya (SPF) za su ba da jagoranci wajen samar da tsaro ga cibiyoyin zaben da kuma kare jami’an hukumar zaben da wakilai, yayin da rawar da AMISOM za ta taka shi ne tallafawa jami’an ’yan sandan na SPF.

Shugabannin kasar Somaliya sun sanar a watan Mayu cewa, za a shirya gudanar da zabukan kasar cikin kwanaki 60 domin kashe wutar rikicin siyasa da ta kunno bayan da shugaban kasar mai ci Mohamed Farmajo ya tsawaita wa’adin shugabancinsa. (Ahmad)