logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 73 a arewa maso yammacin Najeriya

2021-09-02 10:11:46 CRI

Da safiyar ranar Laraba wasu gungun ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 73 a makarantar kauyen Kaya dake karamar hukumar Maradun a jahar Zamfara, kakakin hukumar ‘yan sandan jahar Mohammed Shehu, ya bayyana cikin wata sanarwa.

Ayuba Elkana, shi ne kwamishinan ‘yan sandan jahar Zamfara, ya fadawa taron ‘yan jaridu a Gusau babban birnin jahar cewa, gwamnatin jahar ta ba da umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun firamare da sakandaren jahar bayan garkuwa da daliban na baya bayan nan.

A cewar kwamishinan, gwamnati ta kuma sanya dokar hana fitar dare a kananan hukumomi 13 na jahar a matsayin matakan kawo karshen karuwar hare haren ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane a jahar.