logo

HAUSA

Najeriya ta doke Cuba da ci 3-2 a gasar FIVB U-19 ta duniya

2021-09-02 10:55:21 CRI

Najeriya ta cimma nasarar farko a gasar kwallon raga ta kasa da kasa ta yara maza ‘yan kasa da shekaru 19, wato FIVB U-19 a Tehran, na kasar Iran, inda ta cimma nasara da ci da 3-2 tsakaninta da Cuba a ranar Laraba.

Musa Nimrod, shugaban kungiyar wasan kwallon raga ta Najeriya yace, yayi farin ciki matuka bisa yadda Najeriya ta samu nasarar farko a gasar a wannan rana. Hakan wasu alamu ne dake nuna cewa akwai makoma mai kyau ga fannin wasan kwallon raga ta Najeriya. Yace yaran sun yi wasan da zuciyarsu da tunaninsu da kuma hannunsu, wanda hakan ya basu nasara a rukuni na biyar.

Nimrod yace, a shekaru biyun da suka gabata, sun kammala wasan a matsayi na 14 a kasar Tunisia, kuma yace ya sha umartarsu dasu yi kokarin lashe wasansu na karshe domin su kai ga cimma nasara a bisa tarihin da magabatansu suka kafa a lokutan baya.(Ahmad)