logo

HAUSA

Zimbabwe ta yaba wa kasar Sin kan kokarinta na yaki da annobar Covid-19

2021-09-01 11:18:54 CRI

Zimbabwe ta yaba wa kasar Sin kan kokarinta na yaki da annobar Covid-19_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_6012_718eab85-fa8e-4716-82eb-1d698448ae74

Ministan harkokin waje da cinikin kasa da kasa na kasar Zimbabwe Frederick Shava, ya fitar da sanarwa a ranar 30 ga watan da ya gabata cewa, yadda ake yunkurin dora wa kasar Sin laifin annoba ba ita ce mafita ba wajen warware matsalar, ya kamata kasa da kasa su hada kansu domin cimma burin kawo karshen annobar, ya kuma nuna yabo ga kasar Sin kan kokarinta wajen yaki da annobar da ma nasarorin da ta cimma.

A game da yadda wasu kasashe suke fakewa da sunan binciken gano asalin cutar don boye gazawarsu wajen shawo kan cutar da ma siyasantar da batun cutar, Frederick Shava ya jaddada cewa, yadda ake neman dora wa kasar Sin laifin annobar ba mafita ba ce. Ya ce, Zimbabwe na kalubalantar sassa daban daban da su martaba kimiyya, sa’an nan su gabatar da ra’ayoyinsu bayan da suka yi nazari da ma samar da shaidu ta fannin kimiyya. Ya nanata cewa, rahoton da tawagar masanan WHO suka gabatar bayan ziyarar aiki da suka kai kasar Sin a watan Maris na bana ya yi nuni da cewa, ba zai yiwu a samo asalin cutar Covid-19 daga dakin gwaji ba.(Lubabatu)