logo

HAUSA

MINUSMA: Fararen hula 527 rikicin Mali ya shafa a rubu’i na biyu na shekarar 2021

2021-08-31 10:53:51 CRI

MINUSMA: Fararen hula 527 rikicin Mali ya shafa a rubu’i na biyu na shekarar 2021_fororder_0831-Mali-Ahmad

A kalla fararen hula 527 ko dai aka kashe, ko aka raunata, ko yin garkuwa ko kuma suka bace a rubu’i na biyu na shekarar 2021 sakamakon keta hakkin dan adam a kasar Mali, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali (MINUSMA), ta bayyana hakan cikin rahotonta na tsakanin 1 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Yunin shekarar 2021, wanda aka wallafa a ranar Litinin.

Galibin keta hakkin fararen hular da aka samu a kasar, kungiyar Jama'at nusrat al-Islam wal Muslimin (JNIM), wato kungiyar IS a babban yankin Sahara (EIGS), ita ce ta dauki nauyin shiryawa, da kuma sauran kungiyoyin makamantanta, wadanda ko dai suka kashe, ko suka jikkata, ko kuma suka yi garkuwa da kashi 54 bisa 100 na mutanen da hare haren suka shafa a duk fadin kasar, MINUSMA ta kara da cewa, kashi 20 bisa 100 na tashe-tashen hankullan sun faru ne sakamakon rikicin masu dauke da makamai na cikin gida da kuma kungiyoyin dake fafutukar kare kansu. (Ahmad)