logo

HAUSA

Masanan Sin da Afrika sun yi taro kan yadda za a kare nau’o’in dabbobin daji

2021-08-31 10:04:01 CRI

Masanan Sin da Afrika sun yi taro kan yadda za a kare nau’o’in dabbobin daji_fororder_0831-Sin-Afirka-dabbobi-Ahmad-namun daji

Kwararrun masana gandun daji na Sin da Afrika sun gudanar da taron dandalin tattauna yadda za a bullo da dabarun kiyaye nau’ikan dabbobin daji.

Taron wanda aka gudanar ta kafar bidiyo da zummar nazari kan yadda za a bada kariya ga dabbobin daji da kuma shahararrun nau’ikan dabbobin wanda kungiya mai rajin kare halittu ta Afrika ACBA, da takwararta ta kasar Sin CSABC suka shirya.

Taron dandalin ya jaddada muhimmancin kiyaye nau’in halittu da muhallansu domin a samu damar kyautata zaman rayuwar al’ummun yankunan karkara. Dukkan masanan na Sin da Afrika sun amince cewa inganta kiwon lafiya, kyautata yanayin tattalin arziki, da hadin kai suna daga cikin muhimman ginshikan fannoni ga al’ummomi wadanda suke da alaka ta kai tsaye wajen baiwa muhallin halittu kariya ciki har da gandun daji. (Ahmad)