logo

HAUSA

UNICEF ta yi maraba da sakin dalibai a Najeriya

2021-08-29 16:10:24 CRI

Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF, ya sanar jiya Asabar cewa, ya yi matukar farin cikin sako dalibai da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantarsu tun watan Mayu a jahar Naija dake shiyyar arewa maso tsakiyar kasar Najeriya.

Abubakar Sani Bello, gwamnan jahar Naija, ya fada a taron manema labaru a Minna, babban birnin jahar cewa, mutanen kimanin 92, da suka hada da dalibai 90, sun samu ‘yancinsu ne bayan shafe tsawon watanni uku a hannun ‘yan bindigar da suka kaddamar da hari a makarantar Islamiyar Salihu Tanko Salihu dake garin Tegina a karamar hukumar Rafi dake jahar tun a ranar 30 ga watan Mayu.

A bayanin da aka fitar a ranar Asabar, Peter Hawkins, wakilin asusun UNICEF a Najeriya, ya ce, UNICEF tana taya iyayen yara daliban da suka samu ‘yanci murna, kana tana nuna juyayi da mika sakon ta’aziyya ga iyalan dalibi guda da ya mutu a hannun masu garkuwar.

Hawkins ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa makarantun kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika musamman a watannin baya-bayan nan.

A cewar jami’in asusun na UNICEF, ilmi shi ne muhimmin ginshiki na hakkokin kowane yaro, kuma duk wani yunkuri na kaddamar da hari kan makarantun ilmi tamkar take wannan hakki ne.(Ahmad)

Ahmad