logo

HAUSA

Mali ta dage takunkuman da ta kakabawa tsohon shugaban riko na kasar da Firaministansa

2021-08-28 17:09:46 CRI

Mali ta dage takunkuman da ta kakabawa tsohon shugaban riko na kasar da Firaministansa_fororder_4bed2e738bd4b31c488c3a6b9c92aa779f2ff87f

Kwamitin kula da mika mulki a kasar Mali, ya yi maraba da matakin gwamnatin riko na kasar, na dage takunkuman da ta kakabawa tsohon shugaban rikon kwarya, Bah N’Daw da Firaministansa Moctar Ouane.

Wata sanarwa da kwamitin ya fitar jiya, ta kuma yi maraba da matakan da gwamnatin ta dauka na tabbatar da sun amfana daga hakkokin da suke da shi a matsayinsu na tsohon shugaban kasa da tsohon Firaminista. (Fa’iza Mustapha)