logo

HAUSA

An saki wasu daliba 32 da aka sace a Nijeriya

2021-08-28 20:49:09 CRI

An saki wasu daliba 32 da aka sace a Nijeriya_fororder_b8014a90f603738d3426b60fabc87259f919ec8f

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da sakin wasu karin dalibai 32 da ‘yan bindiga suka sace daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist ta jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, an saki daliban ne a jiya Juma’a, inda ya ce ko a makon da ya gabata a ranar 21 ga wata, an saki wasu daliban makarantar 15. (Fa’iza Mustapha)