logo

HAUSA

Kungiyoyi masu zaman kansu na Sin da Afirka sun yi kira da a kawo karshen wariyar launin fata game da rabon alluran riga kafin COVID-19

2021-08-28 16:22:54 cri

Kungiyoyi masu zaman kansu na Sin da Afirka sun yi kira da a kawo karshen wariyar launin fata game da rabon alluran riga kafin COVID-19_fororder_src=http___images.shobserver.com_news_690_390_2021_8_19_b5f9cb7582dd47d59c9b2e8a5d10bc50&refer=http___images.shobserver

Shugaban kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama’ar kasar Sin Lin Songtian da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu 22 daga kasashe 19 na Afirka, sun rattaba hannu tare, kan wata wasika da suka rubutawa Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, inda suka yi kira ga hukumar da rike ruhin kimiyya da kwarewa da kuma gaskiya, wajen aiwatar da ayyukan gano asalin cutar COVID-19, kana ta yi adawa da sanya siyasa da bata suna a fannin, da kuma nuna fifiko da goyon bayan Afirka wajen tinkarar annobar.

Wasikar ta ce Amurka ta gaza shawo kan yaduwar cutar a cikin kasarta yadda ya kamata, ta kuma kasa dakatar da yaduwar cutar zuwa wasu kasashe, balle ma ta taimakawa wasu kasashe, ciki har da kasashen Afirka wajen yakar cutar, inda kuma take kokarin siyasantar da yanayin annobar.

A cewar wasikar, abin damuwa shi ne, ci gaba da yaduwar annobar na matukar barazana ga rayuwar jama’ar Afirka, da kuma haifar da mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, har ma da yin cikas ga saurin tasowar kasashen Afirka. Dukkan kungiyoyin, sun yi kira da babbar murya da a kawo karshen wariyar launin fata kan rabon alluran riga kafin, da daukar kwararan matakai don tallafawa Afirka, suna masu cewa, ta hakan za a iya taimakawa Afirka wajen tinkarar annobar. (Mai fassara: Bilkisu)