logo

HAUSA

Tawagar wakilan Sin dake AU ta mika alluran rigakafi ga kwamitin AU

2021-08-27 14:26:32 CRI

Tawagar wakilan Sin dake AU ta mika alluran rigakafi ga kwamitin AU_fororder_hoto

Jiya Alhamis, tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, ta mika alluran rigakafin cutar COVID-19 ga kwamitin kungiyar AU. Mr. Chen Xufeng, mukaddashin shugaban tawagar wakilin kasar Sin dake AU, da Mr. Bankole Adeoye, wakilin kula da harkokin siyasa da zaman lafiya na kwamitin kungiyar AU ne suka sa hannu kan takardar mika alluran rigakafin.

Mr. Bankole Adeoye ya ce, a halin yanzu, kasashen Afirka suna fama da matsalar karancin alluran rigakafi, inda kasar Sin ke ba su goyon baya matuka a fannin yaki da annobar. Ya kuma jaddada cewa, kungiyar AU tana goyon bayan aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19 bisa ilmin kimiyya.

A nasa bangaren kuma, Mr. Chen Xufeng ya ce, tallafin alluran rigakafin da kasar Sin ta samar wa kwamitin kungiyar AU za su taimakawa jami’an kwamitin da jakadun kasashen Afirka dake kungiyar AU wajen yin rigakafin cutar COVID-19.

Ya kara da cewa, bayan barkewar annobar, kasar Sin ta samar da tallafin alluran rigakafi ga kasashen Afirka 47, wadanda suka nuna bukatar gaggawa. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da mai da kasashen Afirka matsayin kasashen dake kan gaba ta fuskar bada tallafin alluran rigakafi. Kuma za ta ci gaba da goyon bayan kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka a fannin yaki da annobar. (Maryam)