logo

HAUSA

UNDP na neman bunkasa dabarun shugabanci a tsakanin mata matasa a Afrika

2021-08-27 14:20:34 CRI

UNDP na neman bunkasa dabarun shugabanci a tsakanin mata matasa a Afrika_fororder_210827-Faeza1

Shirin raya kasashe na MDD UNDP, ya sanar da wani shirin tallafi ga mata matasa 25 domin bunkasa dabarunsu na shugabanci.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a Nairobi, babban birnin Kenya, shirin UNDP ya ce yana tafiyar da shirin mai taken African Young Women Leaders Fellowship Programme a karo na biyu da hadin gwiwar hukumar kula da Tarayyar Afrika AUC, domin inganta daidaiton jinsi a harkar shugabanci.

A cewar UNDP yayin wa’adin shirin na watanni 12, za a tura mahalartansa zuwa hedkwatar AUC dake Habasha da birnin New York, ko kuma daya daga cikin ofisoshin hukumar na yanki ko wata kasa.

Manufar shirin ita ce, samar da wani rukunin da ya hada kwararrun mata matasa da za su ingiza kirkire-kirkire da ci gaba mai dorewa ta hanyar musayar dabarun ci gaba tsakanin kasashe masu tasowa. An bude shirin ne ga ‘yan asalin kasashe mambobin AU wadanda suka kai shekaru 34 kuma ba su shiga karo na farko na shirin ba. (Fa’iza Mustapha)