logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 7 kuma ta raba wasu 74,000 da muhallansu a arewacin Najeriya

2021-08-27 10:22:26 CRI

Kimanin mutane 7 ne suka mutu kana wasu mutane 74,000 sun kauracewa muhallansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta faru cikin wannan wata a jihar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi a yankin suka bayyana.

Mohammed Sulaiman, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, ya fadawa manema labarai a Yola, babban birnin jihar cewa, ana ci gaba da fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a jihar, inda kawo yanzu lamarin ya shafi al’ummomin yankuna 79 a kananan hukumomin jihar 16.

A cewar jami’in, ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da dama da dubban hektoci na gonakin noma, inda aka tafka hasarar dukiyoyi miliyoyin naira da suka hada da dabbobin gida.

Ya kara da cewa, ambaliyar ruwan da aka samu ta baya bayan nan a jihar Adamawa ta faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.

Dama dai, hukumomi a Najeriyar sun yi gargadi a watan Mayu cewa, akwai yiwuwar jihohi 28 cikin jahohin kasar 36 da babban birnin tarayya, za su fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a wannan shekara.(Ahmad)