logo

HAUSA

Adadin mutanen da COVID-19 ta kashe a Afrika ta kudu ya zarce 80,000

2021-08-26 09:42:23 CRI

Adadin mutanen da COVID-19 ta kashe a Afrika ta kudu ya zarce 80,000_fororder_0826-S.Africa-Ahmad

Sama da mutane 80,000 sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar cutar COVID-19 a kasar Afrika ta kudu tun bayan barkewar annobar a watan Maris na shekarar 2020, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NICD ta sanar da hakan.

Cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kasar ta samu adadin mutane 516 da suka mutu a sanadin cutar COVID-19 wanda shi ya kawo adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar a kasar zuwa 80,469. Haka zalika, an samu sabbin mutanen da suka kamu da COVID-19 a kasar kimanin 13,251 cikin sa’o’i 24, wanda shi ya kawo jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar zuwa 2,722,202.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar zagaye na uku na barkewar annobar nau’in delta. Sai dai kuma, an samu raguwar alkaluman sabbin masu kamuwa da cutar a lardin Gauteng mafi yawan jama’a a makonnin baya bayan nan, yayin da lardin KwaZulu-Natal (KZN) ya kasance wajen da sabon nau’in cutar ta COVID-19 ya fi kamari.

“Adadin da aka samu a yau ya zarce na jiya kuma ya zarce adadin da aka samu na sabbin masu kamuwa cutar a kullum cikin kwanaki 7 din da suka gabata. Adadin da ake samu na kamuwa da cutar a kullum ya ragu," a cewar hukumar ta NICD. (Ahmad Fagam)