logo

HAUSA

Yawan masu kamuwa da COVID-19 a Afrika ya doshi miliyan 7.6

2021-08-26 10:12:49 CRI

Yawan masu kamuwa da COVID-19 a Afrika ya doshi miliyan 7.6_fororder_0826-cases-Ahmad

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika ya kai 7,592,195 ya zuwa yammacin ranar Laraba.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika ta ce, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar ya kai 191,048 a fadin nahiyar.

Hukumar ta ce, ya zuwa yanzu, jimillar majinyatan da suka warke daga cutar ya kai 6,717,483 a nahiyar.

Afrika ta kudu, Morocco, Tunisia da Habasha suna daga cikin kasashen Afrika mafi yawan masu kamuwa da cutar a nahiyar, kamar yadda hukumar ta bayyana.

A cewar hukumar, kasar Afrika ta kudu ce ke da adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar a nahiyar Afrika inda take da jimillar 2,708,951, yayin da kasar Morocco ta arewacin Afrika take da yawan masu kamuwa da cutar 821,129, ya zuwa yammacin ranar Laraba.

hukumar ta Afrika CDC ta bayyana cewa, game da yawan alkaluman kamuwa da cutar kuwa, kudancin Afrika ne shiyyar da annobar ta fi shafa, sai arewaci da gabashin nahiyar, yayin da tsakiyar Afrika ce shiyya mafi karancin masu kamuwa da cutar. (Ahmad)