logo

HAUSA

Nijeriya ta amince da amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin cikin gaggawa

2021-08-25 10:41:16 CRI

Nijeriya ta amince da amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin cikin gaggawa_fororder_0825-6

Hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko ta Nijeriya, ta ce hukumomin sa ido na kasar sun amince da amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin a matakin gaggawa.

Shugaban hukumar Faisal Shuaib, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi jiya a birnin Abuja cewa, hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya ta gama bincike na karshe kan riga kafin, inda ta amince da yin amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin a Nijeriya a matakin gaggawa. Wannan ne karo na farko da Nijeriya ta amince da alluran rigakafin cutar COVID-19 na Sin.

Rahotanni na cewa, an fara yin alluran rigakafin cutar COVID-19 a zagaye na biyu a kasar a ranar 16 ga wannan wata. Burin gwamnatin Nijeriya a wannan fanni shi ne, yi wa kashi 40 cikin dari na dukkan mutanen kasar da suka cancanta allurar, kana zuwa karshen badi kuma, adadin ya kai kashi 70 cikin dari. (Zainab)