logo

HAUSA

Labarin zuriyoyi uku masu kiyaye muhallin halittu a yankin Saihanba

2021-08-25 14:50:19 CRI

Labarin zuriyoyi uku masu kiyaye muhallin halittu a yankin Saihanba_fororder_779

A baya yankin Saihanba ya kasance cike da hamada, amma mutanen zuriyoyi uku masu kiyaye muhallin halittu a wannan wuri sun kwashe shekaru fiye da 50 wajen dasa itatuwa, har ya zama daji mafi fadi da bil Adama ya dasa a duniya. A shekarar 2017, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga daukacin al’umma da su bi tunanin raya tattalin arziki tare da kiyaye muhalli don yayata ruhin Saihanba. A ranar 23 ga watan Agustan bana, shugaban ya kai ziyara dajin, lokacin da ya yi hira da ma’aikata masu kula da dajin, ya nanata cewa, dole ne a yayata ruhin Saihanba don kara karfin kiyaye muhalli.

A shekarar 1962, aka kafa rukunin dasa daji a Saihanba mai mambobi 369, wadanda matsakaicin shekarunsu bai kai 24 ba, daga cikinsu akwai Zhao Zhenyu, wanda bai dade da gama karatunsa daga makarantar koyon ilmin sha’anin noma na birnin Chengde a waccan lokaci ba. Sun sa kaimi ga kiran da Sin ta yi don hana yaduwar hamadan, hakan ya sa suka zama zuriya ta farko da ta fara wannan aiki.

“Da farko ba mu fahimci wahalhalu masu tsanani da za mu fuskanta ba. A lokaci mafi sanyi digiri zai kai -43.5℃, idan ba a shirya sosai ba, za a ji rauni.”

Amma, duk da ganin wadannan wahalhalu, Zhao Zhenyu ya kwashe shekaru fiye da goma, wato shekaru mafi kyau a rayuwar mutum, yana aiki a nan, ban da wannan kuma matarsa ita ma tana aiki a wannan wuri, lamarin da ya sa ba su iya kula da yaransu sosai ba, amma ba su yi nadama ba ko kadan, a ganinsa aikin kiyaye muhalli da hana yaduwar hamada aiki ne mai matukar muhimmanci, kuma idan babu sadaukarsu, ba za a iya dasa wadannan bishiyoyi ba.

Aikin dake ke kan gaba a wannan wuri shi ne hana tashin gobara. Masu kiyaye daji su kan ce, ginin Wanghailou idon daji ne. Yu Cheng mai shekaru 57 a duniya, yana aiki a cikin wannan gini har shekaru 20, mahaifinsa na daga cikin zuriya ta daya ta dasa bishiyoyi, kuma shi ya fahimci cewa, aikinsa shi ne kiyaye dajin da mahaifinsa ya dasa. Ya ce:

“Akwai kadaici sosai a wannan wuri, aikina akwai wahala sosai duk da cewa yanzu ana kyautata yanayin aikinmu, saboda duk mintoci 15 muna sanar da ko akwai gobara ko babu a cikin sa’o’i 24 ta wayar tarho, muna kwashe sa’o’i 19 a ko wace rana wajen buga waya.”

Matarsa Wang Shaoxian ta biyo Yu Cheng zuwa wannan wuri, don kiyaye daji da kula da iyalinsu. Ta ce:

“Ya kan yi sintiri a dare, ni kuma na yi da safe, alhakinmu ne, dole ne mu kiyaye. Danmu ya na neman aiki a nan bayan ya dawo daga rundunar soja, amma diyyarmu ba ta son wannan wuri.”

Zou Jianming, da aka haifa a shekarar 1989, na daga cikin zuriya ta uku dake gudanar da wannan aiki, ya saurari labaran mahaifinsa da kakansa tun lokacin da yake karami, a wani lokaci ya kan yi fushi matuka saboda mahaifinsa ba ya komawa gida saboda dimbin ayyuka. Amma, bayan ya girma, yana fahimtar aikin da mahaifinsa ya yi, hakan ya sa ya karbi wannan muhimmin aiki daga mahaifinsa bayan ya gama karatunsa a jami’ar koyar da ilmin noma na lardin Hebei. Ya ce:

“An haife ni a nan, na girma a nan. Duk wani itace mahaifina da kakana da abokan aikinsu ne suka dasa. Yana da muhimmanci mu kiyaye su tare da gadon wannan aiki daga zuriya zuwa zuriya, wannan alhaki ne dake wuyan zuriyarmu.” (Amina Xu)