logo

HAUSA

Ministocin lafiya a Afrika sun lashi takobin hada hannu wajen yaki da COVID-19

2021-08-25 09:28:47 CRI

Ministocin kasashen kudu da hamadar Sahara, sun yi alkawarin bunkasa yaki da cutar COVID-19 ta hanyar inganta shirin rigakafi da musayar dabaru.

Da suke tattauna yayin taron kwamitin hukumar lafiya ta duniya na Afrika, ministocin sun ce dakile annobar shi ne jigon farfadowar tattalin arzikin nahiyar.

A cewar ministan lafiya na Cote d’Ivoire, Pierre Ngou Dimba, ya ce nahiyar na iya kawar da mummunan tasirin cutar, idan aka inganta yi wa jama’a allurar rigakafi da farfado da cibiyoyin lafiya da kuma kiyaye matakan kandagarkin cutar.

Ya ce bincike cikin hadin gwiwa da inganta sa ido da gwaji da samar da jinya a kan kari, za su karfafa karfin kasashen nahiyar na shawo kan annobar.

Sama da wakilai 400, da suka hada da ministocin lafiya da wakilan hukumomin kasa da kasa da malamai da kungiyoyin al’umma ne suka halarci taron da aka yi ta kafar bidiyo.

Taron na ministocin lafiya na kasashen Afrika na farko da aka fara jiya, zai gudana ne har zuwa gobe, inda zai tattauna sabbin dabarun bunkasa yaki da COVID-19 da kiwon lafiya ta kafar intanet da kawar da cutar sankarar mahaifa da inganta lafiyar tsoffin dake nahiyar. (Fa’iza Mustapha)