logo

HAUSA

Yawan wadanda cutar kwalara ta halaka a Najeriya ya karu zuwa 1,768

2021-08-24 21:16:24 CRI

Yawan wadanda cutar kwalara ta halaka a Najeriya ya karu zuwa 1,768_fororder_242dd42a2834349ba909a84d1efef5c637d3be8d

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana Talatar nan cewa, tun lokacin da cutar kwalara ta barke a kasar a watan Janairu zuwa yanzu, cutar ta halaka mutane 1,768.

Babban jami’in cibiyar, Chike Ihekweazu, ya bayyana cewa, rashin ruwan sha mai tsafta da al’ummomi a yankunan karkara ke fuskanta, da rashin ma’aikata da za su yi aikin dakile cutar, gami da rashin isassun alluran riga kafin cutar da za a aika zuwa yankunan kananan hukumomin kasar da cutar ta shafa, na daga cikin kalubalolin da ake fuskanta wajen dakile cutar.