logo

HAUSA

Dakarun tsaron Najeriya sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a arewa maso yammacin kasar

2021-08-24 09:53:03 CRI

Sojojin Najeriya sun yi nasarar wargaza wani yunkurin ‘yan bindiga na yin garkuwa da mutane inda suka kubutar da mutane 15 a jahar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda jami’ai a jahar suka bayyana.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da al’amurran cikin gida na jahar, yace dakarun tsaro sun kaddamar da hari kan motoci biyu dake dauke da gungun ‘yan bindigar a ranar Lahadi a kauyen Jagindi dake karamar hukumar Jema'a a jahar, a lokacin da ‘yan fashin suka yi yunkurin garkuwa da fasinjoji 15 yayin da suke kan hanyarsu.

Aruwan yace, bayan da dakarun sojojin suka samu kiran waya ta neman agaji, tawagar dakarun tsaron musamman ta Operation Safe Haven sun gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru. Sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, tare da kubutar da mutanen da aka yi yunkurin garkuwar dasu.

A watannin baya bayan nan, Najeriya tana samun yawaitar hare haren kungiyoyin ‘yan bindiga, lamarin da ke sanadiyyar kashe rayukan mutane da yin garkuwa da wasu. (Ahmad)