logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kashe jami’an soja biyu a Najeriya

2021-08-24 21:14:18 CRI

Mai magana da yawun makarantar horas da kananan hafsoshin soja ta Najeriya dake Kaduna(NDA) Bashir Jagira, ya bayyana cewa, an kashe wasu jami’an soja biyu, kana an yi awon gaba da guda daya da sanyin safiyar Talatar nan, lokacin da wani gungun ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari a makarantar, dake jihar Kaduna a yankin arewa maso yammacin kasar.

Bashir Jagira, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, ‘yan bindigar sun shiga makarantar ce a ranar Talata da safe, bayan da suka samu muhimman bayanai game da matakan tsaron makarantar.