logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a arewa maso yammacin Nijeriya

2021-08-24 09:57:53 CRI

Rundunar ‘yan sanda Nijeriya ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50, biyo bayan harin da suka kai jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu, ya ce da yammacin ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga masu yawa a kan babura, suka yi wa garin Goran Namaye dake yankin karamar hukumar Maradun na jihar tsinke, inda suka yi ta harbin mazauna.

Mohammed shehu, ya bayyanawa wani taron manema labarai a birnin Gusau cewa, an tura jami’an ‘yan sanda yankin domin tabbatar da tsaro, yana mai cewa, ana gudanar da aikin bincike da ceto domin kubutar da mutanen da aka sace.

Ana samun jerin hare-haren ‘yan bindiga a Nijeriya a watannin baya-bayan nan, lamarin dake kai wa ga asarar rayuka da sace-sacen mutane. (Fa’iza Mustapha)