logo

HAUSA

Dan kunar bakin waken IS ya kai hari shingen binciken jami’an tsaro a kudancin Libya

2021-08-23 10:06:42 CRI

Wani maharin kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci ta IS a ranar Lahadi ya kaddamar da hari kan shingen binciken jami’an tsaro mallakin sojoji masu sansani a gabashin Libya a kauyen Zalla dake kudu maso gabashin kasar.

Ahmad al-Mismari, kakakin sojoji masu sansani a gabashin kasar ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, maharin kungiyar IS ya kaddamar da harin bam a cikin mota a sansanin binciken jami’an sojoji na Zalla, amma ba a samu hasarar rai ba.

Ya kara da cewa, an mayarwa maharin martani inda aka ji masa mummunan rauni, daga bisani ya mutu a asibiti.

Al-Mismari ya wallafa wasu hotuna dake nuna yadda jini ke kwarara daga raunukan dake jikin maharin.

Tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011, Libya take fama da matsalolin rashin tsaro da tashe-tashen hankula. (Ahmad)