logo

HAUSA

An saki dalibai 15 da aka sace a Nijeriya

2021-08-23 11:00:36 CMG

An saki dalibai 15 da aka sace a Nijeriya_fororder_0823-Kaduna-faiza-1

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da sakin dalibai 15, daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka sace daga wata makaranta a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya ce an saki daliban na makarantar sakandaren Bethel Baptist ne a ranar Asabar da dare, bayan sun shafe kwanaki 48 a hannun ‘yan bindiga.

Daliban da aka saki na daga cikin wadanda aka sace da ba a san adadinsu ba, daga makarantar Bethel Baptist dake yankin karamar hukumar Chikun ta jihar a ranar 5 ga watan Yuli.

Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista reshen jihar Kaduna, John Joseph Hayab, ya shaidawa manema labarai cewa, akwai sauran dalibai 65 da ke hannun ‘yan bindigar, kuma kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki na tattaunawa da ‘yan bindigar. (Fa’iza Mustapha)

Bello