logo

HAUSA

An kashe fararen hula 19 a harin jamhuriyar Nijer

2021-08-23 09:45:35 CRI

An kashe fararen hula 19 a harin jamhuriyar Nijer_fororder_210823-ahmad-1-Niger

A daren Asabar, ma’aikatar harkokin cikin gida da tsaron al’umma ta jamhuriyar Nijer ta sanar da cewa, an kashe fararen hula 19 tare da raunata wasu mutane 2 a wani harin da ’yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kaddamar a kauyen Tem dake Anzourou a yammacin yankin Tillabery a Juma’ar da ta gabata.

A ranar Larabar da ta gabata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya taba yin Allah wadai da babbar murya game da wani hari daban da ’yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kaddamar kan fararen hula a yankin a Litinin makon jiya.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, Guterres ya nuna matukar damuwa game da yawaitar hare-haren da ake kaiwa kan al’umma duba da yanayin tsananin bukatar tallafin jinkan bil adama da ake fama da shi a yankin, da ma tun tuni akwai mutane sama da 100,000 da rikici ya raba da muhallansu, kana sama da mutane 520,000 ne ke bukatar tallafin jin kai a yankin , a cewar kakakin.

Babban sakataren ya jaddada aniyar MDD na ci gaba da taimakawa Nijer a kokarin da take yi na yaki da ayyukan ta’addanci da hare-haren masu tsattsauran ra’ayi, domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da samar da dawwamamman cigaba. (Ahmad)