logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kai hari wani gari a jihar Zamfara tare da yin garkuwa da sama da mutane 70

2021-08-22 17:06:12 CRI

图片默认标题_fororder_微信图片_20210822170538

A cewar rahotanni daga kafafen yada labaran Najeriya, a ranar 20 ga watan Agusta, wasu gungun mahara sun kai hari garin Rini, a yankin karamar hukumar Bakura a jahar Zamfara, dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 70.

A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 da rabi na safiyar ranar 20 ga wata. Wasu ‘yan bindiga sama da 100 akan babura sama da guda 50 ne suka shiga garin. Mazauna garin sun buya a cikin gidajensu bayan da suka ji karar harbe harbe, to sai dai maharan sun dinga bi gida-gida suna kwankwasa kofa tare da yin awon gaba da mutanen.

Mohammed Shehu, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce adadin ‘yan bindigar ya zarce 60, kuma akwai bukatar a kara tantance yawan adadin. Haka zalika, Mohamed Shehu yace, a kokarinsu na kubutar da mutanen, an kara tura jami’an ‘yan sanda masu yawa zuwa yankin don ceto mutanen.(Ahmad)

CRI