logo

HAUSA

Najeriya zata ba da tukuici ga ‘yan wasan kasarta da suka yi fice a gasar cin kofin duniya ta U20 championships

2021-08-22 16:23:40 CRI

Najeriya zata ba da tukuici ga ‘yan wasan kasarta da suka yi fice a gasar cin kofin duniya ta U20 championships_fororder_1000

Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa zata bayar da kyautar kudi ga ‘yan wasan kasar da suka lashe lambobin yabo a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 wato Under-20 Championships wanda ke gudana a birnin Nairobin kasar Kenya.

Za a bayar da kyautar dala 5,000 ga wadanda suka lashe lambar yabo ta zinare, sannan dala 3,000 ga wadanda suka samu lambar yabo da azurfa, sai kuma dala 2,000 ga ‘yan wasan da suka lashe lambar yabo ta tagulla, ministan matasa da cigaban wasannin na kasar Sunday Dare, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ministan yayi alkawarin bayar da kyakkyawar sakayya ga ‘yan wasan da suka nuna bajinta tun gabanin fara wasannin.

A karshen wasannin na kwanaki 4 a gasar kwararrun ta tsawon kwanaki biyar, Najeriya ta yi nasarar lashe lambobin zinare uku da tagulla biyu.

Bayan samun lambobin, Najeriya tayi nasarar kaiwa mataki na uku a cikin jerin kasashe mafiya samun lambobin yabo inda take bin bayan kasar Kenya mai masaukin baki da kuma Finland.(Ahmad)