logo

HAUSA

Togo ta karbi kashi na biyu na gudunmawar riga-kafin COVID-19 daga Sin

2021-08-22 16:42:16 CRI

Togo ta karbi kashi na biyu na gudunmawar riga-kafin COVID-19 daga Sin_fororder_微信图片_20210822164148

Kasar Togo ta amshi kaso na biyu na gudunmawar riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac daga kasar Sin, a matsayin wani bangare na hadin gwiwar kasashen biyu wajen dakile yaduwar annobar ta COVID-19.

Jakadan kasar Sin a Togo, Chao Weidong, da ministan lafiyar Togo Moustafa Mijiyawa, sun karbi alluran riga kafin a filin jirgin saman kasa da kasa na Gnassingbe Eyadema da yammacin ranar Juma’a.

Jakadan ya ce, wannan gudunmawar riga-kafin, zai taimakawa kokarin da gwamnatin Togo ke yi wajen fadada shirinta na yiwa al’ummar kasar riga-kafin domin baiwa al’ummarta garkuwa daga kamuwa da annobar.

Mijiyawa ya yabawa kasar Sin bisa gudunmawar da ta baiwa kasarsa. Inda ya bayyana cewa kashin farko na gudunmawar alluran riga-kafin da kasar Sin ta baiwa kasar an yi amfani da su ne wajen yiwa daliban jami’o’in gwamnatin Togo biyu, yace kasar Togon zata yi kyakkyawan amfani da wadannan alluran riga kafin.

A ranar 23 ga watan Afrilu kasar Togo ta karbi kashin farko na riga-kafin kamfanin Sinovac wanda kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmawa. Kawo yanzu, kasar ta yammacin Afrika tana da jimillar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar 19,128, yayin da cutar ta hallaka mutane 172 tun bayan samun rahoton farko na bullar cutar ta COVID-19 a kasar a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2020.(Ahmad)