logo

HAUSA

An kashe fararen hula 19 a harin Nijer

2021-08-22 21:18:20 CRI

Ma’aikatar harkokin cikin gidan da tsaron al’umma ta jamhuriyar Nijer ta sanar da cewa an kashe fararen hula 19 tare da raunata wasu mutane 2 a wani harin da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kaddamar a kauyen Tem dake Anzourou a yammacin yankin Tillabery.

Harin, wanda aka kaddamar kan fararen hula a ranar Jumma’a da misalin karfe 9 na dare a lokacin da suke yin salla, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Ma’aikatar ta sanar da cewa, an kara tura jami’an tsaro zuwa yankin, kana ana gudanar da bincike domin bankado wadanda suka shirya wannan kazamin harin kana muggun laifi na bata gari.

A shekarun baya bayan nan, yankin yana kara fuskantar munanan hare hare wadanda ke haddasa hasarar rayukan dakarun tsaron kasar da fararen hula.(Ahmad)