logo

HAUSA

Jaridar Herald ta Zimbabwe: Amurka na fakewa da batun binciken asalin cuta domin cimma muradun siyasa

2021-08-20 19:12:07 CRI

Jaridar Herald ta Zimbabwe: Amurka na fakewa da batun binciken asalin cuta domin cimma muradun siyasa_fororder_cuta

Jaridar Herald da ake wallafawa a Zimbabwe, ta ce Amurka na fakewa da batun binciken asalin cutar COVID-19 domin cimma muradun siyasa. Makalar da jaridar ta wallafa a ranar Laraba, ta ce kamata ya yi kasashen duniya su nuna kin amincewa da siyasantar da batun binciko asalin wannan cuta, kuma hadin gwiwar sassan kasa da kasa ne kadai, zai tabbatar da nasarar yaki da wannan annoba.

A wani ci gaban kuma, ita ma jaridar Singapore Straits Times, ta ranar Talata, ta ce a baya bayan nan an samu adadin mutane har 1,000 da cutar COVID-19 ta hallaka a Amurka. Kaza lika a tsakanin watan guda, matsakaicin adadin masu rasuwa a duk rana a kasar ya kai mutum 769, wanda shi ne adadi mafi yawa da kasar ke samu, tun daga tsakiyar watan Afirilu.  (Saminu)